WASHINGTON D.C —
Mu’azam Umar mawaki da ya shafe shekaru bakwai yana waka, ya ce yanayin rayuwa ne ya sa ya fara waka, mussamam ma halin da matasa suka tsinci kansu na shaye-shaye.
Ya ce ruwan da ya dake ka shine ruwa, a halin da ake ciki matasa basu sami kyakkyawan tushe ba wanda ya jefa yawanci cikin halin ha’ula’I a fannoni na zama koma baya a cikin alumma.
Mawakin ya kara da cewa an bar matasa a baya a harkar demokradiya da harkokin ciyar da kasa gaba, kuma, basu da ta cewa a cikin alu’umma.
Mu’azam ya ce abin takaici ne yadda matsa suka tsunduma cikin harkar shan kwayoyi, bangar siyasa da dukkanin wasu abubuwan da basu dace ba.
A cewarsa ta hanyar waka yana isar da sakonninsa ga matasa domin su gyara rayuwarsu.