Kamfanin Facebook ya fitar da sabbin hanyoyi da zasu taimaka wajen dakile yada labaran bogi da wasu ke kafewa a kafar sadarwar.
Shugaban kamfanin Mark Zuckerberg, yayi alkawarin ganin ya shawo kan lamarin ta hanyar gano duk wadanda ke kafe ire-iren labaran bogi, yayin da ake ‘kara samun tashin jijiyoyin wuya kan yawan karuwar labaran karya a shafukan yanar gizo.
Dandalin Facebook dai na cikin tsaka mai wuya, bayan da ake zargin cewa an kafe labaran karya domin ganin an sauya akalar sakamakon zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar.
Cikin ire-iren labarun akwai wani labari dake cewa an biya wani mutum kudi har $3,500 domin ya tayar da tarzoma a wani taro da zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi a baya. An dai kafe wannan labari ne da sunan wani shafin yanar gizo na bogas na ABC News.
Labarin dai ya yadu sosai har ofishin kamfen din Donald Trump ya dauka da zargin Hillary Clinton da yin amfani da kazaman hanyoyi wajen batawa ‘dan takararsu suna.
A duk lokacin da aka kafe irin wannan labari yakan yadu cikin gaggawa, kuma ba wai yana yada labarin karya bane kadai, har ma yana samarwa da ‘yan damfarar kudin shiga. Damuwa da yadda labaran ke bata sunan Facebook a idon duniya, Mark Zukerberg, ya kafe a shafinsa cewa kamfanin yana daukar labaran boge bada wasa ba.
Cikin sabbin hanyoyin da kafanin ya dauka don dakile faruwar hakan har da saukakawa mutane yadda zasu mikawa kamfanin rahoton ganin labaran boge, da amfani da wasu kamfanonin waje don tabbatar da sahihancin labari da kuma kafe gargadi a labaran da aka tabbatar basu da sahihanci.