Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Matasa Sun Yunkuro Domin Maido Da Cikakken Zaman Lafiya A Jihar Adamawa


Yayin da ake kokarin samar da zaman lafiya a wasu yankunan jihar Adamawa, yanzu haka wasu kungiyoyin matasa a jihar sun yunkuro domin maido da cikakken zaman lafiya a yankin Numan da ya sha fama da tashe tashen hankula a baya.

Matasan sun ce dole a tashi tsaye wajen kawo fahimtar juna da daidaito a tsakanin al’ummun yankin wato Bachama da Hausawan da aka Haifa a yankin.

Na baya bayannan shine wani taro da kungiyar matasan Bachama suka gudanar har suka bada lambar yabo ta zaman lafiya a yankunan.

Mr Efremo Paul Turaki, shine shugaban kungiyar matasan ‘yan kabilar Bachama ya bayyana cewa yanzu lamurran sun koma kamar yadda suke da farko ba tare da nuna wariya ko kyamar juna ba.

Shima wani shugaban kungiyar matasa a bangaren Hausawa, Alhaji Suleman M. D, ya ce zasu cigaba da wannan yunkuri na wayar da kan matasa a yankin domin samun dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG