Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Hango Wasu Duniyoyin Wata, Dake Boyo Bayan Taurari!


Jerin wasu masana binciken sararin samaniya, a kasar Brazil, sun yi wani sabon hange, a cewar shugaban binciken, Farfesa Jorge Melendez, na tsangayar binciken sararrin samaniya, a Jami’ar kimiyya da fasaha ta Sao Paulo, a kasar Brazil. Sun iya hango wasu duniyoyin wata guda biyu, biyo bayan irin wannan nasarar da su kayi irinta a shekarar da ta gabata. Suna dai kiran wadanan duniyoyin da suna “Super Neptune” da “Super Earth.”

Inda suka gano wata duniyar watan wada take kama da duniyar wata na “Jupiter” a cewar jaridar “G1News” ta kasar Brazil, ta ruwaito farfesa Jorge, na cewar, babban burin su shine su zurfafa bincike, a wannan duniyar ta sararin samaniya don kara fahimtar yanayin duniyar.

Sun iya gano cewar rayuwa a duniyar wata, mai dauke da yanayin da suke kira HIP 68468, yana da wuya, domin kuwa ba kowane irin na’ura ce zata iya zuwa wajen ba, balle har suga irin yadda yanayin wajen yake. Wannan yanayin na HIP 68468, yana hadiye wasu duniyoyin na wata, a sanadiyar karfin wani sinadari, da ke narkar da wasu abubuwa cikin gaggawa.

Taurari basu da karfin hadiye wata karamar hallita. Duk dai da cewar duniyar tana zagayawa kusa da taurari, wanda hakan na nuni da cewar, suna yawo daga wani bangare zuwa wani, don haka shi yasa suke ganin wadannan sababbin duniyoyin da suka gano a matsayin wani cigaba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG