Rabon Najeriya, ta cin wasa a waje irin wanda tayi tsakanin ta da Zambia, tun shekarar 2014, Hon Isa Musa Matori, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Wikki tourist dake garin Bauchi, ne ya bayyana haka a wata hira da Dandalinvoa.
Ya ce Najeriya, muna da ‘yan wasa kwararro gida da waje wadanda zasu iya zuwa ko ina a duniya su taka leda matsalar da ake samu shine wajan zaben wadanda yakamata a zakulo su bugawa kasar wasa.
Ya kara da cewa yanzu Alhamdulillahi sabin masu horas da ‘yan wasan da aka dauka da kuma hukumar kwallon kafa ta (NFF) sun fahinci cewa dole a hada karfi da karfe a cire son zuciya da kabilanci in har ana son wasan kwallon kafa ta ci gaba a Najeriya.
Kuma da izinin Allah Najeriya, zata cire kitse a wuta kuma zata je gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, haka kuma zata baiwa marada kunya domin zata yin rawar gani feye da yadda ta taka a gasar cin kofin kwallon kafa na shekarar 1994 da akayi a kasar Amurka.
Batun samun nasara a wannan rukunin da Najeriya,ta tsinci kanta rukunin da ake mata take na mutu wanda ta hada da Najeriya, Morocco Algeria da kuma Zambia dukanin wadannan kasashe kowa yasan kowa domin mukan shasu a gidansu suma suna shanmu a gidan mu amman a wannan karon banaji akwai wata kasa da zata iya taka mana birki a wannan rukunin ba, saboda irin ‘yan kwallon da muke dasu koda a cikin kasashe goma ne ake bukatar daya tak to bana shakku zamu iya zama na daya kuma gashi mun samu shugaban kasa Muhammad Buhari yana taimakawa kwarai.
Game da sabon mai horas da Kungiyar ta Super Eagles kuwa Gernot Rohr dama Najeiya, bawai matsalarta mai horas wa bane a'a matsalar ita ce baza a bari a zabe ‘yan wasan da suka dace ba sai kowa ya kawo nasa ko bai daceba ya ce dole sai anyi dashi amma yanzu Alhamdulillahi kar kashin jagoran shugaban hukumar NFF na kasa Mr Amaju Pinick a na kokarin kawar da wannan dabi'a.
WASHINGTON, DC —