WASHINGTON, DC —
Shugaban hukumar kwallon kafa na Afirka, (CAF) Issa Hayatou, ya kara jaddada cewar ba za’a kara yawan kungiyoyin kwallon kafa masu fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ba (AFCON).
Akwai kiraye kirayen cewa a kara kungiyoyi takwas akan kungiyoyin goma sha shida dake fafatawa a gasar AFCON, kamar yadda UEFA tayi a gasar zakarun turai.
Hayatou, yace ba zai yu a kara yawan kungiyoyin dake buga wasan a gasar ba domin rashin isassun filayen wasa kamar kasashen Turai, ya kamata muyiwa kaimu adalci.
Shugaban ya kara da cewa a lokacin daya hau kujeran shugabancin kungiyar,kungiyoyi takwas ne suka zamo goma sha biyu a shakarar 1992,sa’ilin nan a shekarar 1996 suka zamo goma sha shida.