Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles dake Nigeria Gernot Rohr ya gayyaci dan wasan gaba na Wikki Tourist dake Bauchi Godwin Obaje zuwa sansanin horo na ‘yan wasan Super Eagles da zasu fafata da kasar Zambia a gasar neman shiga gurbin cin kofin duniya na shekarar 2018.
Obaje shine dan wasan da yafi kowa zurara kwallaye a gasar NPFL ta shekarar 2015/2016, inda ya zurara kwallaye har guda goma sha takwas a wasanni daban daban.
A yanzu haka mutane 7 ne kacal suka samu isowa sansanin a cikin manyan ‘yan wasan da aka gaiyata masu taka leda a kasashen waje mutanen sun hada da Carl Ikeme, Elderson Echiejile, Musa Mohammed, sai Ikechuku Ezenwa, Emmanuel Daniel, Bobby Clement tare da Ogenyi Onazi Inda ake sa ran isowar danwasan Gaba na Man City Kelechi Iheanacho a yau.