Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Enugu Rangers Ta Lashe Gasar


Enugu Rangers
Enugu Rangers

Kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers ita ta samu nasaran lashe gasar a bana karo na bakwai kenan Rangers ta na daukan gasar na Nigerian League sai dai rabon Kungiyar ta lashe irin wannan kofin tun shekara ta 1984 kimani shekaru 32, kenan Rangers, ta samu nasaran ne a wasanta na karshe da tayi a gidanta ranar lahadi 2/10/2016 tsakaninta da Kungiyar El-kanemi inda ta lallasa El-kanemi da ci 4 da nema.

Wannan yabata damar haurawa mataki na daya da maki 63, inda tasamu tikitin zuwa Champion league na kasashen Africa, `Rangers ta fafata wasanni har guda 36, a gasar professional league, tayi nasara a wasanni guda 18, tayi kunnen doki sau 9, an doke ta sau 9, a cikin wasannin da tayin ta samu daman zurara kwallaye har guda 53, ita kuma aka zurara mata guda 37.

Itama kuwa Rivers United ta karkare ne a mataki na biyu inda tayi wasanni guda 36 ta samu nasara a guda 19, tayi kunnen doki 3, aka doke ta a wasanni guda 14, itama tanada maki 60, daidai da kuma kwallaye 38, ita kuma an zurara mata kwallaye 29, a ragarta Itama tasamu damar wakiltan Nigeria, a gasar champion league na Afirka.

Wikki tourist na jihar Bauchi ita take matake na uku yayin da tayi wasanni 36, tasamu nasara a 16, tayi kunnen doki 9, an kuma doke ta sau 11, itama tasamu wannan nasara ne a ranar lahadi 2/10/2016 inda ta lallasa takwaranta sunshine da ci 2 da nema a filin wasa na Sir Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi.
Wikki tasa kammala wasanta da maki 57, da kwallaye 45, inda itama aka zurara mata kwallaye har guda 28, a yanzu haka itama ta samu tikitin confederation Cup.
A kasar teburin kuwa na professional league 2015/2016 kungiyoyi guda uku sun yanki tikitin koma kasa da wasan NPFL kungiyar sune Ikorodu United da Warri Wolves sai Giwa FC wanda tuni da ma ita hukamar da take kula da wasannin league na Nigeria (LMC) ta dakatar da ita bisa karya dokokin da tayi.

Ita kuwa Heartland, har yanzu bata san makomantaba sakamakon hatsaniyan da ya tashi a wasansu na karshe tsakanin su da Plateau United, inda wasan ya tsaya a 1-1 a can garin Jos, a ranar Lahadi yanzu haka ana sauraron hukuncin da LMC zasu yanke kafin susan matsayinsu na ko sun haye ko kuma akasin haka.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG