WASHINGTON DC, —
A kowane irin wasa ko sana’a, akwai abun da ake kira kaddara
ko tsautsayi. Tsautsayi da karar kwanaki sun kai ga
shahararren dan wasan “Boxing” dan kasar Scotland a
yankin kasashen turai.
Dan wasan boksin Mike Towell, ya rasu ne bayan garzayawa
asibiti da akayi da shi, biyo bayan wasan da suka gwabza da
abokin karawar shi. Dan wasan mai shekaru ashirin da biyar
da haihuwa, a zagaye na biyar dan wasan ya jikkata, lokacin
da suke karawa da dan wasa Dale Evans.
Mai dakin dan wasan ta bayyanar da cewar, mijin nata
ya mutu cikin sauki, da kwanciyar hankali, haka kuma duk
dangin shi suna kusa da shi a dai-dai lokacin da rai yayi halin
shi.
Ta kara da cewar, dama dai duk cikin ‘yan kwanakin nan, yayi
ta fama da wani matsanancin ciwon kai, wanda yayi jinya
na kwanaki da dama. Amma wannan wasan nashi, shine
ya zama sanadiyyar mutuwan shi, suna mishi fatar ya huta.