Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Dutse Ya Goyi Bayan Hukumar Kiyaye Hadurra Ta Kasa Ta Bada Lasisin Tukin Babur A Jihar


Rahotanni sun bayyana cewa sarkin Dutse Alhaji Nuhu Mummad a wata ganawa da ya yi da sabon kwamandan jami’an kiyaye hadurra ta kasa yayin da yake ziyara a ofishin sa, ya bukaci hukumar ta fara ba masu tuka babur a daukacin fadin jihar lasisin tuki.

Sarkin ya yi jawabin cewa yawancin masu tuka Babura a jihar basu da kwarewa musamman masu tuka baburan haya ko Achaba, ya kara da cewa yawancin ‘yan achabar dake tuka Babura a jihar basu iya ba, da dama kwarewarsu bata kai yadda zasu hau babbar hanya ba, dan haka ya ce ya goyi bayan yi masu lasisin tuki.

Ya kara da cewa yawancin su basu iya tuki ba, ya kamata a tantace kwarewar su kuma za’a iya yin hakan ta wajan kungiyar matuka baburan domin babu shakka yin hakan zai rage yawan hadurran da ake samu a jihar.

Daga karshe ya bayyana cewa yawancin 'yan achaban jihar suna mugun gudu da fasinjoji, kuma yawanci sai sun yi shaye shaye kana suke tukin, lamarin da a cewar sa ya ke ci masu tuwo a kwarya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG