A yau mun sami bakuncin mawaki Ibrahim D Ibrahim, wanda aka fi sani da Babangida – Gagas, wanda ya zabi waka a matsayin sana’arsa.
Ya ce sakamakon turban da ya zaba, ya fuskanci kalubale da dama , inda sana’ar sa ta sa ya kusa rasa auren da yake nema a cewar iyayen wacce yake so ba zai iya rike musu diya ba da sana’ar wakar da yake yi.
Mawakin ya kara da cewa mutane na yi wa mawaka kallon kaskanci da rashin fahimta, domin kuwa a cewar sa waka tayi masa komai a rayuwa, kuma yana alfari da sana’ar sa domin dukkani rayuwa ana gina ta ne a turbar soyayya, kuma fannin da ya fi raja’a a wakokinsa kenan
A fannin mu na tsegumi kuwa, a yau ne fitattacen jarumin nan na Nollywood Mie Ezuruonye, ke bikin ranar haihuwarsa, shi ma fitattacen mawaki Shaydee, na gudanar da nasa bikin ranar haihiwa.
An dai haifi Shaydee a garin Kano inda yayi karatunsa na digiri a garin Ilorin, ya kuma karanci aikin Injiniya.
Za kuma ku ji muhawarrar da ake fafatawa a shafukan facebook na shin tsakanin dafadukan shinkafa, wato Jollof-rice ta kasar Ghana da ta Nijeriya wacce ta fi dadi?.
Saurari rahoton Baraka Bashir.