A jiya ne haddaiyar kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa wato MOPPAN Motion pictures practitioners assocation of Nigeria reshen jihar Kano suka gudanar da zaben su inda Kabiru Mohammad Maikaba ya lashe zaben ya zama shugaban kungiyar , Hafizu Bello mataimakinsa Salisu Mohammad Sakatare inda Balarabe Murtala Baharu jami'n hulda da jama'a na kungiyar.
A hira ta mussamam da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, ya ce lokaci yayi na fara magance matsalolin da ke addabar masanaantar Kannywood da suka dangance yi wa sana'ar hawan kawara.
Yana mai cewa kalubalen da yake gaba masana’antar fina finai ba karami bane kuma babban matsalar da take fuskantar masana’antar yanzu shine rashin fahimtar sana’ar ga wasu daga cikin al’uma da kuma duruwar ta bayan gida da wasu keyi domin shigowa cikin sana’ar batare da bin kaidar sana’ar ba masamman mata.
Ya kara da cewa da dama wasu na shigowa masana’antar ne da wata manufa ta daban don haka daga wannan lokacin wannan abin an kawo karshe domin za’a tabbatar da tsarin yadda za’a shiga sana’ar fim kamar yadda shugabanin baya suka yi kokari mu tabbatar.