Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Idon Mage Ya Waye A Soyayyar zamani - Inji Matasa


Yayin da iyaye ke kokarin ganin sun yi bakin kokarinsu musamman wajan tabbatar da cewa 'ya'yansu sun sami abokan zama na kwarai ta fannin auratayya, wasu da dama cikin samari da 'yan mata na ganin cewa lamarin daban yake da yadda yake a da.

Dalilin wannan kuwa shine, dandalin voa ya sami zantawa da samari da 'yan mata da dama domin jin ra'ayoyinsu akan tambaya kamar haka; sa hannun iyaye wajan nemawa 'ya'ya aure, taimako ga makomar aure mai nagari ko hana ruwa gudu?.

Matasa da dama sun bayyana ra'ayoyinsu akan wannan lamari, kodashike kashi tamanin da shidda cikin dari na matasan da muka sami Zantawa dasu sun nuna cewa lallai zamani ya canza, dan haka aure awannan zamani ana yinsa ne domin soyayya ba domin arzikin da wani bangare keda shi, ko ilimi ba, amma ginshikin shine sayayya tsintsa domin haka "idon mage ya waye".

Akwai dalilai da dama da kan yi sanadiyyar aure tsakanin matasa a wannan zamani kamar su karatu a makarnta guda, zama unguwa guda ko dangantaka da juna ko ta hanyar mu'amula da abokai da sauran su.

Abin tambaya anan shine, wacce hanaya ce tafi zama mafi dacewa kuma a ina domin haduwa da abokan soyayya?

Kubiyo mu a shirinmu na sati mai zuwa domin in amsoshin wadannan tambayoyi a shafinmu na dandalivoa.com da kuma shafinmu na facebook domin jin amsoshin wadannan tambaoyi da kuma bayyana ra'ayi.

XS
SM
MD
LG