Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa matasa guda tara ne suka rasa rayukan su a yayin da suke gudanar da bukukuwan sallah a sakakamakon tattake su da aka yi a wurin da ake gudanar da wasannin.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar laraba bayan an gama hawan idi, inda matasa suka shirya wasanni a wani zauren taro kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar Ashanti ASP Yusuf Tanko ya bayyana cewa,
“a yayin da suke gudanar da taron, akwai ‘yar hayaniyar data tashi a tsakanin matasan kuma ba’a san ainihin abinda ya haifar da matsalar ba, sai wani daga cikin su ya kashe fitilar dake wurin, ta dalilin haka ne tsoro ya shige su, sai suka fara gudun neman hanyar fita gashi kuma kofar guda ce ta inda ake shiga ta nan ake fita, to wadanda suka fadi wajan gudun sune aka tattake har tara daga cikin su suka rasu, wasu guda takwas kuma na asibiti a kwance”.
Da sashen Hausa ya tambaye shi ko jami’an tsaro sun leka wannan wuri a yayin da matasan ke gudanar da taron? Kakakin jami’an ‘yan sandan ya amsa cewa sukan tura ma’aikatansu a duk inda ake gudanar da wani taro, amma ma’aikatar tsaron bata san cewar matasan nada taro a wannan rana kuma a wannan wurin ba.
Shugabannin musulmi sun dade suna kira ga matasan jihar Ashanti da su kaucewa shirya wasannin gargajiya musamman wadanda suka sabawa addinin musulunci.
Ta dalilin haka ne sarkin zango sultan Umar sa’id ya bayyana cewa irin wadannan wasannin basu kamata ba.
Saurari cikkaken rahoton anan.