Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Lionel Messi Da Mahaifin Sa Daurin Watanni 21


Kotu ta yankewa shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya wanda ya ajiye takalman bugawa kasar sa wasa Lionel Messi, dan shekaru ashirin da haihuwa hukuncin daurin watanni ashirin da daya da shi da mahaifin sa, da kuma tarar kudi Euro miliyan biyu, sa’an nan mahaifin kuma Euro miliyan daya.

Wannan hukunci da kotu ta yanke ya biyo bayan kama dan wasan da mahaifinsa ne da laifin kin biyan kudin haraji a kasar Spain akan dukiyar da dan wasan ya mallaka.

Lionel Messi ya bayyanawa kotu cewa bashida masaniya akan kin biyan gwamnatin kasar Spain kudin haraji domin a cewar sa, kwallon kafa ta kawo shi kasar Spain kuma mahaifinsa ne ke daukar dawainiyar kular masa da duk wani abin da ya shafi dukiyar sa, sai dai yakan sa hannu akan duk takardar da mahaifin nasa ya kawo masa ba tare da ya duba ba domin ya yarda da mahaifin nasa.

A bangaren mahaifin na Messi, shi kuma ya bayyanawa kotu cewar yana da karancin sani akan lamarin, dalilin da yasa hakan ta faru Kenan.

Kodashike kwanakin baya mai shari’ar ya bayyana cewa za’a gudanar da bincike kuma idan aka sami Messi da laifi, babu wata kariya da dan wasan zai samu da zata hana a zartar masa da hukunci.

Dan wasan dai ya shiga kungiyar Barcelona ne a shekarar 2004, kimanin shekaru goma sha biyu da suka gabata Kenan, kuma ya buga wasanni 348 inda ya jefa kwallaye 312.

Lionel Messi ya zamo gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya har sau biyar, kuma yana daya daga cikin masu kudin duniya a bangaren 'yan wasa. Sai dai a irin hukuncin kasar ta Spain, ba lallai ne yayi zaman gidan kaso ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG