Zirga zirgan motoci sun tsaya cik a wasu sassa na birnin Nairobi kasar Kenya, yau Laraba a yayinda daruruwan lauyoyin Kenya suka yi jerin gwano domin nuna rashin amincewar su ga zargin cewa yan sanda sun harbe wani abokin aikin su da wasu mutane biyu.
Jerin gwanon daya kai masu zanga zanga harabar kotun kolin kasar da ofishin specta janaral na yan sandan kasar, shine irinsa biyu da aka yi a wannan makon a birnin Nairobi, domin nuna rashin amincewa ga kashe wani lauya mai suna Willie Kimani da wanda yake karewa da kuma direban taxi din su.
Lauyoyin sunce suna son so jawo hankalin jama’a cewa ba zata sabu ba, bindiga a ruwa, ba zasu yadda ana kaiwa lauyoyi hare hare ba.
Bincike gawarwarki da aka yi ya nuna cewa sai da aka nakadawa mutane uku dukka, sa’anan aka shake su kafin aka kashe su.