Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Jam’iyar Republican A Majalisar Amurka Sun Fusata Akan Batun Hilary Clinton


James Comey
James Comey

Gobe Alhamis idan Allah ya kaimu za’a yiwa daraktan FBI Mr Carney tambayoyi a Majalisa

Wakilan jam’iyar Republican a Majalisar wakilan Amurka da suka fusata, suna shirin yiwa direktan hukumar binciken aikata laifuffuka ta Amirka FBI James Carney tambayoyi masu tsanani gobe Alhamis akan shawarar daya yanke, cewa ba zai bada shawarar a caji tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da aikata laifi ba, a saboda amfani da akwatin sakonin radin kanta wajen gudanar da harkokin gwamnati a lokacinda take mukamin sakatariyar harkokin waje.

A yayinda gobe Alhamis idan Allah ya kaimu za’a yiwa Mr Carney tambayoyi, an shirya a makon gobe idan Allah ya kaimu, yan Majalisar zasu yiwa Atoni Janaral Lorreta Lynch tambayoyi akan wannan batu.

Kakakin Majalisar wakilai Paul Ryan yace tana yiwuwa an nunawa Hillary Clinton gata a binciken da hukumar FBI ta yi mata.

Yace shi yana ganin an nuna so kai ko kuma an nuna mata gata. Mr Ryan yace ya kamata jama’a su san yadda ko kuma abinda yasa direktan na hukumar FBI ya yanke wanna shawara.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG