Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yiwa Rasha da Gwamnatin Syria Kashedi


Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Tun ba yau ba kasashen Amurka da Tarayyar Turai suke korafin cewa Amurka da Syria suna yiwa yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin kasar Syria zagon kasa saboda har yanzu basu daina kai hari kan Aleppo, birni mafi girma a Syria

Amurka tana kashedi ga Rasha da Syria cewa hakurinta yana da iyaka, daga nan tayi kira ga kasashen su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma wacce take tangal-tangal.

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, yana zargin Rasha da gwamnatin Syria, da zabin bangaren yarjejeniyar da zasu mutunta,yayind a dakarun kasar suke ci gaba da kai farmakin domin katse birnin Aleppo, birni mafi girma a kasar, kuma wuri da hukumar kula da al'adun gargajiya wato, UNESCO ta ayyana a zaman wuri na tarihi.

Mr. Kerry yace, mun bayyana a fili cewa, idan ba anyi mana bayani dalla-dalla kan manufar tsagaiata wutar ba, yadda dokar zata yi aiki, yadda za'a aiwatar da ita, wadanda zata shafa, da yadda zata shafe su, ba zamu ci gaba da zura ido muna gani shugaba Assad yana ci gaba da farmaki kan birnin Aleppo, yayinda Rasha take goyon bayan wannan mataki," inji shi.

Da alamun dai yarjejeniyar tsagaita wutardata fara aiki cikin watan Febrairu ta ruguje,babu wani ci gaba da ake samu na gudanar da shawarwari na kafa gwamnatin wucin gadi da ake fatan zai fara aiki daga daya ga watan Agustan bana.

XS
SM
MD
LG