Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Yi Abin Tarihi


Hillary Clinton
Hillary Clinton

Ta zama macce ta farko da wata babbar jam'iyyar siyasa ta tsaida a matsayin 'yar takarar shugaban kasa

Jiya Talata, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta yi abin tarihi inda ta zama macce ta farko da wata babbar jam'iyyar siyasa ta tsaida a matsayin 'yar takarar shugaban kasa. A zaben fitarda gwani da aka gudanar a jiyan, abokin takarar ta Bernie Sanders, ya sami nasara a jihohin North Dakota da Montana, yayinda Clinton ta lashe jihohin South Dakota da New Mexico da kuma New Jersey. Haka kuma Hilary ta lashe jiha mafi girma da aka yi zaben a cikinta, watau jihar California. Bayan nasarar, Hillary tayi wa magoya bayanta jawabi:

Tace: Muna gode muku da kuka taimaka muka yi abin tarihi, inda, a karon farko a tarihin Amurka, macce ce 'yar takarar shugaban kasa na wata babbar jam'iyya."

Sai dai kuma abokin takarar nata, Bernie Sanders har yanzu yaki bada kai, bori ya hau, yace ba zai janye takarar tashi ba duk da cewa ta fi shi yawan kuri'u:

Mr. Sanders yace: "zamu ci gaba da fafatawa, zamu ci gaba da bada kokari don lashe zaben fitar da gwani na birnin Washignton, DC, sannan mu dauki yaki zuwa Philadelphia ta jihar Pennsylvania."

Shima dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar republicans, Donald Trump, ya lashe zaben da aka gudar a dukkan jihohin na jiya, sai dai kuma yana ci gaba da fuskantar kalubale saboda kalaman batuncin da yayi kan wani alkali Ba'amurke, da Trump ya jadadda cewa ai dan Mexico ne:

Trump yace: Kullum burina shine in hada kawunan mutane amma fa idan aka kure ni akan wani abinda yake da muhimmanci a wurina, zan ja daga, in kare matsayina."

Shugaba Obama ya kira duka yan takarar biyu na jam'iyyarsu ta Democrats jiya Talata, inda ya jin-jinawa Hilary Clinton don nasarar samun wakilan da ake bukata a jam’iyyar don tsayawa takara. Haka kuma ya yaba wa sanata Bernie Sanders don fadakar da miliyoyin Amurkawa da yayi akan batutuwa kamar yakar bambance-bambancen tattalin arziki tsakanin al’umma.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG