Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Ta Cafke Wasu Sojojin Kungiyar Hadin Kan Afirka


Wasu cikin sojojin kungiyar Afirka dake Somalia
Wasu cikin sojojin kungiyar Afirka dake Somalia

Sojojin kungiyar hadin kan Afirka guda biyar ne jami'an Somalia suka cafke suna zarginsu da yin kokarin sayar da wasu makaman yaki a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar

Sojojin Somalia tare da hadin kan sojojin kungiyar hadin kan Afirka dake kiyaye zaman lafiya a kasar suka kai samame wani garajin da wasu sojojin kungiyar Afirkan ke kokarin sayar da kayan yaki da suka hadamakamai da kayan kariya.

Kungiyar Tsaron Hadin Kai ta Afirka, ko AMISOM a takaice, dake Somalia tace sam bata amincewa da kowane irin rashin da'a cikin dakarunta. Ta sha alwashin yiwa duk wanda aka sameshi da laifi hukunci. Kungiyar tace ba zata yadda wasu su karkata hankalin dakarunta su 22,000 a Somalia ba. Zasu yi aikin da ya kawosu kasar yadda aka tsara masu.

To saidai kungiyar ta ki ta bayyana kasashen da sojojin biyar da suka shiga hannu suka fito.

XS
SM
MD
LG