Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Kafawa Mutanen Yankinta Dokoki Masu Tsanani Don Ramadan


Mayakan ISIS
Mayakan ISIS

Kungiyar ISIS ta kafa dokoki masu tsanani kan mutanen dake yankunan da take da iko a kasashen Syria da Iraq

Wadannan matsanancin dokokin sun hada da hada yin anfani da tasoshin talibijan daga satellite, takaita sa'o'in aiki da fito da wasu sabbin tsarin tufafi da mata zasu iya sawa.

Kwana kwanan nan kungiyar ISIS ta kaddamar da kemfen tana gargadin mutann Syria da Iraq su fasa akwatunan talibijan dinsu da naurar da suke kama tasoshin waje ta satellite, domin, wai suna kawowa mutane yaki da daular da suka kafa a zuciyarsu.

A wani bidiyo da ta fitar kungiyar tace talibijan na kawo masu muryoyin da suka ki jinin muslmai har cikin gidajensu lamarin da yake cimma muradun makiya inji ISIS.

A birnin Raqqa wanda ya kasance babban birnin ISIS a Syria kungiyar tana bi gida gida tana kwace duk wani talibijan na satellite da wasu naurorin samun labarai daga waje. Duk wadanda ta kama tana yi masu yankan rago ba tare da yin wani shela ba kamar yadda take yi da kamar yadda wata kungiya mai sa ido akan cin zarafin mutane da ISIS keyi a kasar Syria.

A kasar Iraq kungiyar ISIS tace ba zata bar kowa ya bar garin Mosul ba sai ya mika akwatunan talibijan dinsu tare da na satellite. Haka kuma 'yansandan ISIS sun tilastawa gidajen gasa burodi su rufe alatilas da rana har sai an gama zaumi.

XS
SM
MD
LG