‘Yan Najeriya sun fara maida martini game da matakin Gwamnatin tarayya na janye Sojoji domin sasantawa da ‘yan tsagerun Niger Delta, dake kai hare hare a cibiyoyin man fetur da yanzu Najeriya ta dogara dashi.
Wasu ‘yan Najeriya, sun bayyana adawarsu da matakin da Gwamnatin Najeriya, ta dauka na janye Sojoji da kuma zama teburin sasantawa da ‘yan kungiyar Niger Delta, dake kai hare hare kan cibiyoyin hakar mai dake yankin na Niger Delta, lamarin da ya haifar da durkushewar kudadaen da Najeriya ke samu sakamakon hakar man fetur a kasuwannin duniya.
Abdulsalam Abubakar, wani mai fafutukarar kare hakkin bil-Adam, yace babu dalilin sasantawa dasu illa kawai a basu wa’adi ne yana mai cewa idan har za’a samu galaba akan ‘yan Boko Haram, ‘yan Avenger ba abinda zasu tsolewa Najeriya idanu bane. Yakamata gwamnati ta aiwatar da abinda lallai zata nunawa duniya cewa ita gwamnati ce akan su.
Sai dai a bangaren sa Malam Abdulsalam Abdullahi, yace yana ganin cewa akwai bukatar zama teburin sasantawa da ‘yan kungiyar domin kawo karshen tu’annatin suke yiwa tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa ba komai ne za’a yi amfani da karfin Soji domin kawo karshen sa ba, akwai bukatar zama domin sasantawa.
Yanzu dai abin jira a gani shine ko matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka zai taimaka wajen kawo karshen hare haren ‘yan bindigan kan cibiyoyin hakar main a kasar.