Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban Ta Sace Wasu Matafiya 17 A Arewacin Kasar


Taliban
Taliban

Wannan ne karu na biyu da Taliban ta sace mutane da dama cikin mako guda

Wasu jami'an yanki a Afghanistan sun ce kungiyar Taliban ta sace wasu matafiya 17 a arewacin kasar da daren jiya Laraba.

Zabiullah Amani, mai magana da yawun gwamnan lardin, ya ce matafiyan, wadanda mazauna gundumar Balkhab ne, na tafiya ne cikin wata mota zuwa hadikwatar lardin Sar-e-Pul lokacin da 'yan Taliban din su ka sace su.

Ya ce shugabannin kabilun yankin na tattaunawa kan bukatar sakinsu.

Wannan ne karu na biyu da Taliban ta sace mutane da dama cikin mako guda. Taliban ta sace wasu matafiya 200 a farkon wannan satin bayan da su ka kafa wuraren duba ababen hawa na bogi a kan babbar hanyar da ke lardin Kunduz. Daga bisani sun saki wasu daga cikin matafiyan amma sun hallaka 17 daga cikinsu.

A halin da ake ciki kuma daruruwan masu zanga-zanga sun taru a Kabul a yau dinnan Alhamis don nuna fushinsu kan sace mutane da kuma kashe-kashen da aka yi a lardin Kunduz. Wata Jam'iyyar siyasa ce ta shirya zanga -zangar bisa jagorancin wani tsohon shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa Amrullah Saleh.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG