Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Cutar Kuturta Na Barna


 cutar kuturta
cutar kuturta

Ko kadan bai dace a nuna wariya ga masu cutar kuturta ba

Duk da cewa ana samun ci gaba wajen yaki da yaduwar cutar kuturta a duniya, a Najeriya, masana harkokin kiwon lafiya, sun ce har yanzu cutar tana yin barna bisa la’akari da yadda yara kanana ke kamuwa da ita.

Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Neja, kuma shugaban kwamitin amintattu, na cibiyar yaki da yaduwar cutar kuturta a Najeriya, Dr. Zagbayi Nuhu, yace a yanzu haka sun dukufa wajen fadakar da jama’a akan mahimmancin zuwa asibiti, da zarar anga alamun kamuwa da cutar.

Yana mai jawo hankalin jama’a cewa duk wanda yaga alamu kuma ya je asibiti akan lokaci, cikin watani tara zuwa goma sha biyu idan aka sha magani za’a samu waraka.

Dangane da matsalar da masu cutar kuturta ke fama da ita na kyama, Dr. Nuhu yace ko kadan hakan bai dace ba domin idan mutun ya warke babu wata illa da zata yiwa dan Adam.

A yanzu dai cibiyar yaki da yaduwar cutar kuturta a Najeriya, ta kaddamar da aikin samar da wani sabon daki na masamman domin duba masu fama da cutar a babbar asibitin kutare na Minna.

Kwamishina kiwon lafiya na jihar Neja, Dr. Mustapha Jibril, yace wannan dakin zai taimaka matuka wajen yakin da ake yi da cutar kuturta.

Cibiyar ta yaki da yaduwar cutar kuturta a Najeriya, ta bayyana bukatar ganin hukumomin a matakai daban daban na Najeriya, dama na sauran kasashen Afirka, su bullo da wani shiri na masamman domin wayar da kan jama’a, akan nuna kyama da wariya da ake yiwa masu fama da cutar kuturta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG