Kasar jamhuriyar Kamaru ta sake tsaurara tsaro akan iyakokinta da makwabtanta, domin kaiwa ‘yan ta’addan Boko Haram, farmaki.
Mai baiwa Ministan tsaron kasar Kamaru shawara a yakin da ake yi da ‘yan Boko Haram, Maiyaki Ibrahim, yace Kamaru, ta dauki wanna mataki ne biyo bayan taron da kasashen dake makwabtaka da tafkin Chadi suka gudanar a Abuja, na cewa ana sonkawo karshen ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Shima kwamandan rundunar dakarun Sojojin kasar Kamaru na mayakan kasa Sunday Umaru, ya tabbatar wa wakilin muryar Amurka Awal Garba, cewa sun kama ‘yan kungiyar Boko Haram da dama wadanda a yanzu haka suna hannu.
Koda yake a ‘yan kwanakin nan maharan Boko Haram, sun yi sanyi wajen kai hare hare a kasar Kamaru, amma hakan ba shine yake nuni da cewa an cimma buri ban a kakkape ‘yan ta’addan Boko Haram, akan iyakokin kasar baki daya.