Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Ta Kai Hari Kan Wani Otel A Somalia


Bam da ya tashi ya sa motoci sun kama da wuta kana mutane sun mutu wasu kuma asun jikata a Otel Ambassador dake Mogadishu, Somalia
Bam da ya tashi ya sa motoci sun kama da wuta kana mutane sun mutu wasu kuma asun jikata a Otel Ambassador dake Mogadishu, Somalia

Shaidun gani da ido a Mogadishu babban birnin Somalia sun ce akalla mutane goma sun rasa rayukansu kana fiye da goma sha biyar suka jikata sanadiyar harin da 'yan ta'adan suka kai kan otel din jiya Laraba.

Wani dan majalisar dokokin kasar, Muhammad Ismail Shuriye, ya shaidawa Muryar Amurka cewa Abdullah Jama Kaboweyne da Muhammad Gure dukansu 'yan majalisar dokoki suna cikin wadanda harin ya rutsa dasu da kuma Abdullahi Hashi dan majalisa na uku da ya jikata.

Wani dan majalisa dake otel din yace yana barci ne a dakinsa lamarin ya auku. Yace fashewar bam din ya girgizashi. Tagar dakinsa da kofa da suka tashi sama kansa suka fado. Ya gudu bayan dakin ne Allah ya tsirar dashi.

Abdullahi Haji Dayib shi ma ya gayawa Muryar Amurka ya ruga asibiti da wani abokinsa da ya jikata inda ya ga motar marasa lafiya ta kawo mutane da dama da suka jikata.

Wani ma'aikacin Muryar Amurka yace ya ga gawarwaki biyar a gaban otel din.

Rahotanni na nuni da cewa bam da ya tashi a wata mota ne yayinda mutane ke sallar magariba ya rutsa da mutane.

Wannan harin da aka kai kan otel din da 'yan majalisar dokokin kasar da jami'an gwamnati ke anfani dashi ya faru ne sa'o'i kadan bayan da jami'an gwamnati suka sanar da kashe wani babban kwamandan kungiyar al-Shabab a wani samame da sojojin kasar suka kai.

Kwamandan mai suna Mhammed Mohamud, wanda aka fi sani da Dulyadeyn shi ne ya shirya harin watan Afirilun shekarar 2015 a Jami'ar Garissa dake kasar Kenya. Harin shi ya yi sanadiyar kashe mutane 148, kusan dukansu dalibai ne.

XS
SM
MD
LG