Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Senegal Ta Daure Hissene Habre Na Tsawon Ransa


Hissene Habre, yana sauraron hukumci a gaban kotu, litinin 30 Mayu 2016
Hissene Habre, yana sauraron hukumci a gaban kotu, litinin 30 Mayu 2016

Wata kotu a kasar Senegal ta samu tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre, da laifuffukan cin zarafin bil Adama da na yaki da kuma gana azaba, sannan ta yanke masa hukumcin daurin rai da rai a gidan kurkuku.

Wakilan Muryar Amurka, Anne Look da Alpha Jallow, sun ambaci babban alkalin kotun ta musamman, Gberdao Gustave Kam, dan kasar Burkina Faso, yana bayyana cewa sun samu Habre da laifuffukan da aka tuhume shi da aikatawa.

"Kotun ta samu Habre da laifin cewa yana da hannu kai tsaye wajen bayarda umurnin tsare mutane, da kashe su, da gana musu azaba da wasu matakan cin zarafin mutanen da aka gano cewa su na yin hamayya da gwamnatinsa," in ji alkalin.

Alkali Kam yace Habre ya jagoranci danniyar da babu kakkautawa ta tsawon shekaru 8. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce a cikin wannan lokacin ya hallaka mutane fiye da dubu 40.

A lokacin da yake fadan irin hukumcin da za a yi ma tsohon shugaban na Chadi, alkali Kam ya ce Habre "ya kirkiro yanayin da ta'asa da yin ganin dama suka zamo tamkar doka. Shine shugaban gwamnatin da ba ta yarda da kowa ba, har ma ta kai yana juyawa kan jami'ansa yana hallaka su."

Mutanen da suka sha azaba a hannun gwamnatin Habre da iyalan wadanda aka kashe sun fashe da kukar murna yau litinin a lokacin da kotun ta ayyana hukumcin daurin rai da rai a gidan kurkuku a kan tsohon shugaban.

Habre dai bai ce uffan ba a cikin kotun. Ya dunkula hannunsa yana gaisuwa ga magoya bayansa a lokacin da ake fita da shi daga cikin kotun.

Habre ya ki yarda ya tashi tsaye ko kuma ya yarda da alkalin kotun a duk tsawon wannan shari'a, inda ya boye idanunsa a cikin wani tabaro mai duhu, ya kuma sanya wani farin rawani ya rufe kai da fuskarsa.

Habre ya tsere ya koma kasar Senegal a shekarar 1990, a bayan da aka yi masa juyin mulki.

An ba lauyoyinsa kwanaki 15 da su daukaka kara idan ba su yarda da wannan hukumcin ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG