A yayin da Najeriyar ke waiwayen irin matsaloli da kuma nasarorin da sabuwar gwamnati ta cimma a shekara daya bayan sauyin mulki zuwa gwamnati mai akidar canji a matakin gwamnatin tarayya, Ana cigaba da samun sauye sauye a wasu bangarori da dama.
Ta dalilin haka ne wakilin sashin Hausa na muryar Amurka ya yi nazarin irin kalubalen da gwamnonin jihohin Taraba da Adamawa suka fuskanta shekara daya da soma wa’adin mulkinsu.
Gwamna Arch. Darius Dickson Ishaku na jihar Taraba ya koka da tashe-tashen hankula wadanda a cewarsa na daga cikin matsaloli da ke tauya kokarin gwamnatinsa na aiwatar da ayukan rayawa da habaka tattalin arziki, yana mai cewa “jama’a su bani zaman lafiya ni kuma na yi masu aiki”.
Shi kuwa gwamnan jihar Adamawa Sanata Mohammadu Umaru Jibirilla Bindow ya ce matsalar da jihar sa ta yi fama da shi, shine na cin hanci da rashawa yana mai gargadin manyan mukarraban gwamnati da shugabannin kananan hukumomi ba zai yi tantama ba wajen mika duk wanda aka samu da hannu a wawurar dukiyar jama’a gaban kuliya ba sai ya jira hukumar yaki da cin hanci ta tarayya ba.
Ga hirar Sanusi Adamu da gwamnonin biyu.