Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Duniya Sun Firgita Kasancewar Donald Trump Dan Takara


Trump ya mamaye yakin neman zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce Shugabannin kasashen duniya da ya tattauna da su sun firgita da kasancewar Donald Trump dan takara a zaben Shugaban kasa na 2016 -- sannan ya caccaki attajirin mai kaushin lafazi.

Da ya ke magana ga 'yan jarida a birnin Ise Shima na Japan da ke gabar teku a yau dinnan Alhamis, bayan kwana guda da fara babban taron shekara-shekara na Shugabannin kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, Obama ya ce duniya ta sa ido sosai saboda, a ta bakinsa, "Amurka ce jagabar inda duniya ta sa gaba."

Trump ya mamaye yakin neman zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican, saboda irin kalamansa masu janyo takaddama musamman game da baki Hispaniyawa da Musulmi. Ya kuma bukaci a janye sojojin Amurka daga Japan da Koriya da Kudu, a kuma karfafa su da makamin nukiliya don kare kansu daga Koriya Ta Arewa.

Obama ya ce wasu Shugabannin kasashe irinsa ba su ma san yadda za su dau irin wadannan kalaman na Trump ba, wadanda ya ce au na nuna jahilcinsa kan harkokin duniya ko, rainin wayo ko kuma neman suna a kafafen yada labaran.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG