Kimanin sama da mutane dubu dari ne ke bi ta kasar nijar, don zuwa kasashen yamma. Da yawa mutane kanyi amfani da barauniyar hanya ta Nijar, zuwa kasar Libiya ko Algeriya, wanda daga nan mutane sai su fantsama zuwa kasashen turai.
Hakan yasa hukumomin kasashen turai sun gana da hukumomin kasar ta Nijar, don fitowa da wata hanya da za’a magance irin wannan matsalar. A kasar nijar dai an ware wasu makudan kudade da za’a yi amfani da su wajen hana irin wannan balaguron. Domin kuwa mutane da dama kan rasa rayukan su a sanadiyar wannan tafiyar ta cikin hamada.
Kungiyoyin kare hakkin dan’adam suna ganin cewar wannan wata ragguwar dubara ce, domin kuwa idan akace an hana mutane wucewa, sai suyi ya Kenan? Za’a barsu ne a cikin jihar ta Agadas.
Suna ganin abu da yafi kamata shine a kokarta wajen ganin an samar da wani tsari wanda za’a dinga amfani da hanyoyi da suka kamata, wajen barin mutane wuce iyakokin kasashen ECOWAS, musamman idan mutun yana dauke da fasfot na daya daga cikin kasashen kungiyar yammacin Afrika.
Hana mutane shawagi a tsakanin kasashen ya sabama yarjejeniyar kasashen ta ECOWAS. Don haka duk wata kasa da take cikin kasashe goma sha biyar na cikin hadaddiyar kungiyar kasashen Afrika, yakamata a basu damar shige da fice. A tabakin Sa’idu Ya’u, mai kula da kare hakkin matafiya ta kungiyar Altenatib. Jihar Agadas na fama da matsalolin rashin tsaro, don haka babu bukatar tara wasu baki a jihar.