Gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya shaidawa Muryar Amurka cewa nakasassu nada gagarumin gudummawar da zaasu bayar wajen cigaban kasa da al'ummarta idan har suka samu ilimi mai inganci.
Yace a halin da suke ciki sun bude makarantu guda uku na kulawa da nakasassu a kowace mazabar sanata dake jihar.
Wadda aka kafa a garin Lafiya ita ce zata zama cibiyar da zata horas da yaro tun yana dan karami har ya kai kusan zuwa shiga jami'a. Kowace irin nakasa ce yaro yake da ita akwai nashi irin ilimin da za'a bashi. Duk yaran dake da nakasa sun zama yaran gwamnati. Gwamnati zata yi masu komi ba tare da iyayen sun biya ko kwandala ba.
Shugaban kungiyar makafin Najeriya na reshen jihar Nasarawa yace kwanan nan ya kammala digirinsa na biyu a jami'a. Yace kodayake shi bai samu aiki ba yayi imanin cewa ba nakasassu ilimi zai basu anfanin dogaro da kansu. Yace illolin bara nada yawa. Akwai reni da wulakanci, amma ilimi zai ba mutum karfin dogaro da akai.
Ga karin bayani.