Kwamandojin 'yan tawayen Siriya da 'yan adawar siyasa, sun tabbatar cewa ba za su yi nasara ba a gwamgwarmaya da makami da su ka yi, na kau da Shugaba Bashar al-Assad, sanadiyyar sa hannun da kasashen Rasha da Iran su ka yi. To amma sun jaddada cewa ita gwamnatin ma ba fa za ta iya kau da su ta kawo karshen boren ba.
Wannan tashin hankalin ya kai ga raba kan kasar, wadda yaki ya daidaita ta yadda babu ma wata alamar za a samu mafita a siyasance ta sake hada kan 'yan Siriyar.
Ta bayan fage kuma, jami'an diflomaiyyar Amurka na matsa lamba ma wakilan 'yan tawayen da su amince a kafa gwamnatin wuccin gadi tare da Shugaba Bashar al-Assad. To amma 'yan tawayen sun yi watsi da wannan shawarar.
"Sam ba zai fa yiwu ba -- bata lokaci ne kawai," abin da wani mamba a babban kwamitin wakilan 'yan tawayen a batun sasantawar ya gaya ma Muryar Amurka kenan. "Assad fa shi ne iyakarmu -- sabanin yadda Shugaba Obama ya dauki batun amfani da makami mai guba a matsayin iyaka, mu ba za mu kitta ba," a cewarsa.
Karo na uku na tattaunawar da ake da zummar kawo karshen yakin da aka shafe shekaru 6 ana yi a Siriyar ya cije a watan jiya, ta yadda gwamnati da 'yan adawa su ka saba kan muhimman batutuwa - mafi muhimmanci ita ce makomar Shugaba Bashar al-Assad.
MDD ta tsai da watan Agusta a matsayin wa'adin kafa gwamnatin ta wuccin gadi, to amma jami'an diflomasiyyar kasashen yamma sun amsa cewa hakan ba zai samu kafin cikar wa'adin ba.