Yayin da wata babbar kotun tarayya dake Lagos, ta yanke hukuncin saukar da tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Muhammad Makarfi, daga shugabancin riko na jam’iyyar PDP, na kasa ta kuma bada umarni maye gurbin sa da Sanata Ali Modu Sheriff, kan mikamin.
Sai ga wata babbar kotun tarayya dake Fatakwal, ta yanke hukuncin daya dakatar da Ali Modu Sheriff, din daga shugabancin jam’iyyar har zuwa lokaci da zata kamala sauraren wata kara dake gaban ta.
Barrister, Abdullahi Jalo, mukaddashin kakakin jam’iyyar PDP, na kasa siyasa ta mutane ne idan ka ga mutun ya tafi kotu bai bi hanyoyin da jam’iya ta shinfida na sasantawa bane, matsayin jam’iya shine inda jama’a suka yi.
Barrister, Aliyu Abdullahi, idan aka sami irin wannan indn kotun masu daraja iri daya suka yake hukunci masu karo da juna, abin dubawea shine shi wace kotu ne tafara yanke hukunci ko kuma Alkalin alkalan kotun na tarayya yayi fasara.
Shi kuwa Barrister Yakubu s. Malumfashi, cewa yayi kundin tsarin mulkin Najeriya, ya bayana cewa duk wani hukunci na kotun tarayya, idan kanna kalubalantar sa saka tafi kotun daukaka kara ta tarayya ne amma ba wai Alkalin alkalai bane zai bada fasara ba.
Yanzu dai rikicin cikin gida na ci gaba da mamaye jam’iyyar PDP, da takai a lokaci guda nada shugabanin na kasa uku, Sanata Ahmad Makarfi. Sanata Ali Modu Sheriff da Sanata Nasir Ibrahim Mantu.