Shugaban hukumar wasani ta matasa a Najeriya, wato YSFON, Alhaji Nasir Yusuf Gawuna, yace akwai bukatar kafanoni masu zaman kansu, dasu hade da hukumar wajan zakulo wa Najeriya, hazikan ‘yan wasa.
Ya bayana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wurin gasar cin kofin kwallon kafa na hafsan Sojojin ruwa na Najeriya, karo na 15, wanda ake gudanarwa a Abuja, tsakanin maza ‘yan kasa da shekaru 14, da mata ‘yan kasa da shekaru 17.
Yace hana matasa gararamba a tituna da sako sako suna neman aikin da babu shi ta hanyar habaka wasani daga tushe shine babbar abinda zai magance wahalhalu da zaman kashe wando dake addabar matasa a yanzu,
Alhaji Nasir Yusuf, yana mai cewa sai an hada karfi da karfe tsakanin kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni da YSFON, wajan sake Alqibla kasar ta bangaren wasani.
Ya kara da cewa “muna sa ran gano ‘yan wasa kamar su Kanu Nwankwo,Tijani Babangida, Emmanuel Amunike, Austin Eguavoen Yakubu Aiyegbeni da wasu ma fitattun ‘yan wasa da suka kasance sun biyo ta YSFON, kafi kaiwa matsayin da suka kai a faggen wasan kwallon kafa.
Yace za’a horas da sabbin ‘yan wasan da aka gano a wasanin da aka yi na tsawon mako daya domin wakiltar Najeriya a wasan Dallas Cup, a Amurka da wani kuma a kasar Norway.