Yau dandalinvoa ya sami bakuncin wani mawaki ne mai suna Ahmad Adam wanda aka fi sani da Raju Karkasara, wanda ya kwashe sama da shekaru goma yana wannan sana'a.
Da farko matashin ya bayyana cewar ya sami kansa cikin wannan sana'a ne a dalilin mu'amula da abokai masu harkar fina finai da wakoki kuma tun daga lokacin da ya fara waka bai taba rubuta waka ba, wato yakan rera waka ne dangane da labarin da yasa shi rera wakar.
Karkasara ya kara da cewa yana rera wakokin fina finai da na siyasa da kuma wakokin buki koda shike ya ce yafi rera wakokin buki akan sauran wakoki.
Daga karshe ya ce abinda yake kaunar yaga ya cimma a rayuwar sa shine, samun karbuwa fiye da yadda yake yanzu, da kuma biyawa dukkan 'yan uwa da abokan arziki bukatun rayuwa domin yana da shi'awar taimaka ma jama'a.
Ga cikakkiyar hirar.