Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Da Malaman Addini A JIhar Kano Sunyi Wani Taron Addu’a


Gidan Makama, Kano
Gidan Makama, Kano

Kungiyoyin addinin musulinci da malamai sun fara gudanar da tarukan addu’o’I na musamman dangane da annobar gobara da ta wakana a wasu kasuwanin Kano da kuma halin matsin tattalin arziki da al’uma ke ciki.

Kungiyar Kadiriya na daga cikin kungiyoyin da suka gudanar da tarukan addu’ar a baya bayan nan, inda akayi karatu da jawaban jan hankali ga jama’ar kasa da shugabanni a matakai daban daban, Shiek Mohammad Nasiru Kabara, shine ya jagoranci taron addu’ar.

Baya ga taron addu’ar na musammam malamai da limamai na ci gaba da tunatar da shugabanni da mabiya kan bukatar kowa ya rinka sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, domin samun mafita da ga halin da al’umma ta shiga.

Kimanin makwanni biyu da suka gabata ne majalisar dokoki ta jihar Kano, ta zartar da wani kudiri dake kira ga al’umma da su tashi tsaye wajen addu’o’in neman mafita daga mawuyacin hali da al’umma ke ciki.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG