Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalolin Dake Jawo Koma Baya A Bangaren Kiwon Lafiya A Najeriya


Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo
Likitoci da maikatan asibiti suna duban mai ciwo

Rashin kayan aiki da kwararrun likitoci a asibitoci, da kuma rashin albashi mai inganci suna cikin manyan matsalolin.

Matsalolin dake kawo nakaso wajen samar da aiyukan lafiya a Najeriya, sun hada da rashin kayan aiki da kwararrun likitoci a asibitoci, da kuma rashin albashi mai inganci.

Likitan dake jagorantar wani shirin kakakin majalisar tarayya Barrister Yakubu Dogara, na tallafawa jama’a, a kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Haruna Kibu, shine ya yi wanna furushin a garin Bauchi.

Ahmed Yarima, Sarkin Malaman Misau, wanda ya wakilcin kakakin majalisar yace yayi ne domin ya agazawa jama’ar, jihar Bauchi, taimako ne da yake yin a kiwon lafiya, babu wasu kudade da ake baiwa ‘yan majalisa na masamman domin taimakon jama’a,.

Tallafawa ta fanin kiwon lafiya , samar da ruwa da gyara makarantu da wakilai keyi suna yi ne a matsayin tallafi babu wani kasafi na masamman da aka yi daga cikin albashi ko alawus, da ake bada wan a saman gari cewa ‘yan majalisu suyi wannan.

Amma in ji cewar mai taimakawa Gwamna jihar Bauchi a fanin labarai da hulda da jama’a, Sabo Muhammad,yace akwai hakki kan wakilan jama’a suin bada tasu gudumawar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG