Ko dai talauci ke sanya barin yaran gararamba kan tituna ko dai wani abune na daban ya dace manya su rika daukan matakan da ya kamata. Irin wannnan yanayi ya sanya wata yarinya Zulaiha yar kimanin shekaru goma, kwato kanta daga wani gida da aka turata a matsayin yar aikin gida, inda har mai gidan ke mata dan karen duka.
Dakta Mairo Mandara itace babbar jami’a dake kula da asusun Bil Gate da Melinda a Najeriya, fadi irin bukatar da yaran Najeriya musammam na yankin Arewa ke da ita wajen abinci mai gina jiki, da kulawa ta musammam.
Irin yanayin da yaran ke shiga na gallaza musu yasa malaman islama kira ga iyaye da su cije wajen kula da yaran nasu da hanasu gararamba ko turasu wasu garuruwa masu nisa da sunan almajiranci don su koyi karatu.
Ko a birnin Abuja da zarar mutum ya tsaya a mota zai ga kananan yara sun runtumo a guje da sunan a taimaka musu da sadaka don samun abinci.
Domin karin bayani.