A yayinda gwamnati da ma kungiyoyi ke fafutikan gano bakin zaren yadda za'a rage yawan yara kanana maza almajiran makarantun allo dake yawon bara a biranen arewacin Najeriya sai gashi wasu iyaye suna tura 'ya'yansu mata kanana zuwa karatu a wasu garuruwa.
A karamar hukumar Kontagora Muryar Amurka ta ci karo da yara kanana mata da aka kawo yin karatun allo. Daya daga cikinsu mai suna Hauwau tace daga kauyen Sabon Rijiya aka kawota.
Malam Aliyu Abubakar malamin 'yan matan yace duk da yake iyayensu na aiko masu da abinci shi ma yana iyakar kokarinshi. Akan kulawa da yake basu yace idan yarinya bata da lafiya ya kan je ya samo mata magani. Dangane da wanka kuma yace idan yarinya bata yi wanka ba to baya nan ne. Ya musanta zargin cewa yana sasu aikace-aikacen da suka fi karfinsu.
Kawo yanzu Malam Aliyu Abubakar yana da yara mata goma sha daya da yake koyaswa.
Muryar Amurka ta zanta da wasu mata dake makwaftaka da makarantar akan rayuwar yaran. Laura Muhammad tace yaran suna cikin wahala domin babu inda ba'a turasu. Su ne zasu je neman ruwa. Su ne zasu je neman itace. Kai yarinya mace wani wuri karantun allo bai dace ba. Tace sun bata tausayi bisa ga halin da suke ciki.
Ita ma Aisha Sani tace suna taimaka masu da abinci da sutura. Tace suna shigowa talla kuma suna shiga gidanta saboda nata yaran da suke biyowa.
Shehun malami Imam Shehu Rimaye jigo a darikar Tijjaniya a jihar Neja ya yi bayanin lamarin a musulunce. Ba daidai ba ne a tara yara mata da basu da kulawar mata ko iyayensu har sai sun je sun nemo abinci bai dace ba. Musulunci ba zai yadda da wannan irin lamarin ba.
Ita ma gwamnatin Neja tace zata yi bincike akan lamarin ta cewar sakataren gwamnatin Alhaji Shehu Dan Yaya. Yace basu da masaniya amma zasu bincika.
Binciken Muryar Amurka ya nuna akwai irin wadannan makarantun da yara mata 'yan kasa da shekaru goma a kananan hukumomin Kwantagora da Mashegu.
Ga karin bayani.