Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar ana cecekuce akan cancantar sabon shugaban majalisar dokokin kasar


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Biyo bayan zaben 'yan majalisar kasa da aka kammala, sabuwar majalisar ta zabi shugabanta wanda ba'a sanshi ba sosai a faggen siyasar kasar.

A Nijar cecekuce ya barke akan cancantar sabon kakakin majalisar dokokin kasar saboda wai ba sananne ba ne a faggen siyasa.

Ta bakin Ouseni Tinni dalilan cecekuce akan sabon kakakin shi ne kakakin bai yi fice ba a fannin siyasar kasar.

Kakakin jam'iyyar MPR Jamhuriya Alhaji Sani Maikaset yace a birnin Kwanni ba'a san sabon kakakin ba. Baya cikin 'yan siyasan da aka sani har da za'a san jarumtakarsa ko kuma kwarewarsa. Su a Kwanni basu yi tsammanin shi ne za'a sa ya zama sabon kakaki ba. Sun kyautata zato jam'iyyarsu za'a ba

A cewar Alhaji Mani na jam'iyyar PNDS Tarayya yace lallai haka ne sabon kakakin bashi da kwaramniyar siyasa kamar sauran takwarorinsa shi ya sa ba'a jinsa. Amma kafin a dorashi a kujerar kakakin majalisa sai da duk jam'iyyoyi suka zauna suka yi shawara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG