Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afrika Ta Gabas Na Ganawa Kan Zaman Lafiya A Burundi


Amma babbar tambaya a nan ita ce, ko shugaba Nkurunziza zai halarci wannan taron na Arusha ko a’a?

A yau Laraba ne shugabannan kungiyar kasashen Afrika ta gabas suke ganawa a birnin Arusha da ke Tanzaniya. Kungiyar wadda ta kunshi kasashen Burundi da Kenya, da Rwanda da Tanzaniya, dakuma Uganda, wadda kuma helkwatarta ke Arusha tana shiga Tsakani a tattaunawar neman sulhu a kasar Burundi karkashin jagorancin shugaban Uganda Yoweri Museveni. Amma har yanzu wannan tattaunawa ba ta haifar da wani sakamakon da aka gani a kasa ba.

Ta yiwu shugabannan na Afrika su sami rahoto daga shugaba Museveni akan irin rawar da ya ke takawa. Amma babbar tambaya a nan ita ce, ko shugaba Nkurunziza zai halarci wannan taron na Arusha ko a’a?

Ministan harkokin wajen Burundi Alain Nyamitwe ya fadawa muryar Amurka cewa mataimakin shugaban kasa na biyu shi ne zai wakilci kasar.
Gwamnatin ta Burundi ta fada a cikin watan da ya gabata cewa za ta yi maraba da duk wani tayi da Afrika ta kudu zata yi akan taimakawa wajen tattauna tsakanin sassan na Burundi.

Ministan na harkokin waje ya ce Afrika ta kudu ta taka muhimmiyar rawa wajen ganawar samar da zaman lafiya da aka yi a karshen shekarar 1999, da kuma farkon shekarar 2000.

XS
SM
MD
LG