Mr. Hollande ya fadi a wani jawabin daya yi yau Juma’a cewa kutsen wata tsabar barazana ce ga kasancewar Mali. Ya kara da cewa Faransa za ta ji rokon Mali na neman taimako bisa sharadin da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya Shinfida.
A jiya Alhamis ne Kwamitin Tsaron yayi wani zama na tattaunawa kan rikicin na Mali, bayan da ‘yan tawaye su ka kama wani muhimmin gari a yunkurin da suke yi zuwa babban birnin kasar ta Kudu. Kwamitin ya bayar da umurnin tura sojojin kasashen waje cikin gaggawa don su dakile wannan matsalar.
Shugaban wuccin gadin Mali Dioncounda Traore ya roki Faransa, wadda ita ta yi wa Mali mulkin mallaka, da ta taimaka masu cikin gaggawa don dakile ‘yan tawayen.