A can baya, Mr. Hollande ya soki yadda ake keta hakkin bil Adama a gabashin kasar ta Kwango, inda ake fuskantar tawaye. Ya bayyana lamarin a zaman wanda ba za a amince da shi ba.
Shugaba Joseph Kabila na Kwango ya gana da Mr. Hollande tun farko a yau asabar din. A jawabinsa wajen bude taron kolin kuma, ya bayyana tawayen da ake yi a gabashin kasarsa a zaman "yaki na rashin adalci" da wasu daga waje suka dora ma kasarsa. Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kasar Rwanda da goyon bayan tawayen da ake yi a gabashin Kwango, zargin da Rwanda ta musanta.
Ana sa ran cewa wannan tawaye da ake fama da shi a Kwango-ta-Kinshasa da kuma halin da ake ciki a kasar Mali, zasu mamaye tattaunawa a wannan taron koli da za a kammala gobe lahadi.
Jiya jumma'a, Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da kudurin da ya share fagen girka sojojin kasashen waje da zasu taimakawa gwamnatin rikon kwarya ta Mali wajen takalar 'yan tawaye masu kishin Islama wadanda suka kwace yankin arewacin kasar.