Jean-Yves Le Drian ya bayyana wannan yau talata ga gidan telebijin na France 2, kwanaki kadan a bayan da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da kudurin da ya share fagen aikawa da sojojin kasashen waje zuwa Mali.
Yace Faransa ba zata tura sojojinta ba, amma zata bayar da tallafin kayan aiki.
Gwamnatin rikon kwarya ta Mali ta bukaci taimakon wadannan sojoji domin su taimaka mata wajen korar kungiyoyin ‘yan kishin Islama wadanda suka kwace arewacin Mali a bayan wani juyin mulkin da aka yi a farkon shekara.
Kudurin na Majalisar Dinkin Duniya ya ba kasashen Afirka ta Yamma wa’adin kwanaki 45 da su gabatar ma Kwamitin Sulhu da dalla-dallar bayanin shirinsu na tura soja da irin ayyukan da zasu yi a Mali. Har ila yau, kudurin ya bukacib babban sakataren majalisar, Ban Ki-moon, da ya samar da kwararru kan tsare-tsaren ayyukan soja da na tsaro domin su taimakawa kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka wajen kafa wannan runduna.