Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farin Dango Su Na Barazana Ga Amfanin Gona A Afirka


Fara tana lalata amfanin gona a kasar Morocco
Fara tana lalata amfanin gona a kasar Morocco

Hukumar Abinci da Aikin Gona, FAO, ta ce yawan farin dango ya ninku har sau 250 a sandin ruwan sama mai yawa da aka samu a daminar bana

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa farin dango zasu iya yin barazana ga amfanin gona da filayen kiwo a yankin arewa maso yammacin Afirka.

Hukumar Abinci da Aikin Gona ta majalisar (FAO) ta ce ruwan sama mai yawa da aka samu a daminar bana ya haifar da yanayi mai kayu na kyankashe 'ya'yan fari, abinda ya sa yawansu ya ninku har sau dari biyu da hamsin a kasashen Chadi, Mali da Nijar.

Babban jami'i mai kula da Alkaluma kan Farin dango a hukumar ta FAO, Keith Cressman, yace watakila nan ba da jimawa ba wadannan fari zasu fara bazuwa zuwa Aljeriya, da Libya, da Mauritaniya da kuma Morocco.
Farin dango a kasar Madagascar
Farin dango a kasar Madagascar

Cressman yace hukumar FAO tana sanya idanu a kan garakan farin dango a Nijar da Chadi, amma kuma ma'aikatan safiyo na hukumar sun kasa shiga yankin arewacin Mali, inda 'yan kishin addini suka kwaci mulki.

Irin wadannan farin dango dake fitowa daga hamada su na iya tashi su yi tafiyar kilomita 150 cikin rana guda. Hukumar Abinci da Aikin Gona, FAO, ta ce garke guda na irin wadannan fari, zasu iya cinye abincin da mutane dubu 35 zasu iya ci a rana guda kawai.

A shekara ta 2005, yankunan Arewaci da Yammacin Afirka sun fuskanci annobar farin dango mafi muni da suka gani cikin shekaru 20. Farin sun lalata amfanin gona, suka jefa miliyoyin mutane cikin ukubar yunwa.
XS
SM
MD
LG