Wakilin Faransa na musamman a yankin Sahel, Jean Felix-Peganon, ya ce kasar Mali ta bukaci kungiyar ECOWAS da ta tura agajin soja domin maido da kwanciyar hankali a kasar, musamman ma domin kwato yankin arewaci.
Jami’in ya fadawa ‘yan jarida cikin daren jiya talata cewar ya samu labarin takardar neman taimakon da Mali ta gabatar din ne a lokacin wata ganawar da yayi da shugaba Blaise Comapore na Burkina Fasso a Ouagadougou.
ECOWAS ta ce a shirye take ta tura rundunar sojoji dubu 3 zuwa Mali, inda masu kishin Islama suke kokarin shimfida yin aiki da irin tasu fassarar ta dokokin shari’ar Islama.
A cikin wannan makon daya daga cikin kungiyoyin ta kwace wani gari, abinda ya kara gusawa da ita ga yankunan da suke karkashin ikon gwamnatin rikon kwarya ta Mali.