Yayin da kwamitocin binciken zanga-zangar ENDSARS da wasu gwamnonin Najeriya suka kafa ke ci gaba da sauraron bahasi daga jama’a, masu kula da al’amura suna tsokaci akan cancanta ko rashin cancantar kafa kwamitocin, da kuma hasashe akan tasirin rahotannin da zasu mika wa gwamnati.
Daya daga cikin abubuwan da ke haddasa rikice-rikice a kasashe masu tasowa kamar Najeriya sun hada da bambancin ra'ayi, addini, kabilanci da kuma rashin jagorancin masu fada a ji daga matakin tarayya zuwa kananan hukumomi.
Yayin da Najeriya ke cigaba da murmurewa daga rikicin ENDSARS, wanda ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Lawan, Ya ce muddun ba a gaggauta samar ma matasa ayyukan yi ba, to wata 'ENDSARS' din ka iya kunno kai.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya ce yana jagorantar wani shiri na tattara bayanan asarar rayuka da dukiya da al'ummar arewa suka yi don neman diyyar da ta kai Naira tiriliyan bakwai.
TAMBAYA: Menene ku ke so a tabo a wannan zaman musayar miyau?
Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya su daina rufa-rufa kan batun kisan gillan da aka yi wa masu zanga a gadar Lekki.
#EndSars: Duk da dokar hana fita da gwamnati ta sanya, mutane sun balle rumbunan abinci na gwamnati a Jos, inda suka yi ta kwasan kayan abinci.
Domin Kari