An jinkirta sanar da sunayen wadanda aka zaɓba don neman kyautar Oscars kusan mako guda daga ranar da aka tsara tun farko saboda gobarar daji da ake fama da ita a California.
Za a sanar da sunayen zababbun ne yanzu a ranar 23 ga Janairu, Hukumar Academy of Motion Picture Arts and Sciences ta fada a ranar Litinin Kamar yadda AP ya ruwaito.
“Muna cikin alhini sosai game da tasirin gobarar da kuma asarar mutane da yawa a cikin al’ummarmu.” In ji Shugaban Hukumar Academy, Bill Kramer, da Shugabar Hukumar, Janet Yang, a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa.
“Hukumar Academy ko da yaushe, tana kasancewa wata kungiya mai hada kai a cikin masana'antar fim, kuma mun kuduri aniyar kasancewa tare a yayin wannan mawuyacin hali.”
Akalla mutum 24 ne suka rasa rayukansu a lokacin hada wannan rahoto.
Hukumar da ke shirya bikin na Oscars ta yanke shawarar soke liyafar shekara-shekara da ake yi wa zababbun mutanen.
Za a gudanar da asalin bikin na Oscars ne a ranar 2 ga watan Maris, 2025 a karo na 97.
Dandalin Mu Tattauna