Majalisar dattawan Amurka ta tabbatar da wani kasafin kudin da za akasha don gudanar da ayyukan gwanati da daren jiya Jumma’a, wanda ya kawar da yiwuwar rufe ofisoshin gwamnati na wuciun gadi sannan yayi nasara akan hammayar ‘yan Democrats akan wannan batu.
An tabbatar da Kudurin dokar bayan da kuri’u aka kada kuri'a 54-46 wanda ya kawar da wani kalubale na tsarin da zai dakatar da mahawara akan matakin wanda ake bukatar akkala kuri’u 60.
Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Jumma’a, tsohuwar shugabar majalaisar dattawan Nancy Pelosi, ta ce “Amurka ta shiga irin wannan yanayi inda aka rufe ofisoshin gwamnati a wa’adin Trump na farko, amma babu abinda wannan dokar mai illa zata yi illa ta dada dagula al’amura.”
Shugaban marasa rinjaye a majalisar datawan bai amsa tambayar da manema labarai suka mishi jiya Jumma,a ba, akan ko yana goyon bayan shugabancin Schumer ko a a.
Trump ya bukaci majalisar ta amince da kudirin kasafin kudin sannan jiya Jumma’a ya yaba ma Schumer akan yadda ya bada goyon bayan shi ga kudirin.
Dandalin Mu Tattauna