Ba kamar makwabciyarta Najeriya ba wadda take fama da bala'in yunwa, Nijar ba ta cikin irin wannan yanayi. Sai dai duk da hakan, akwai wasu da suka nuna alamun cewa akwai yunwa kuma lamarin ka iya karuwa saboda matsalar fari musamman a yankin Diffa.
Kone konen da kungiyar Boko Haram ta dinga yi a jihar Borno sun sa jihar ta shiga wani halin fari na bazata da yunwa saboda baicin karuwar kwararowar hamada yawancin jama'ar jihar basu iya fita zuwa noma ba
Yankin arewa maso gabas ya fada cikin wani halin fari saboda kara kwararowar hamada sanadiyar rikicin 'yan Boko Haram da yawan sare itatuwa domin yin makamashi da su
Akalla mutane 489 sun mutu sanadiyar barkewar annobar sankarau a Najeriya, a cewar ministan lafiyan kasar Isaac Adewole.
Rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba dake Arewa maso Gabashin Najeriya na nuni da cewa yanzu haka ana fama da matsanancin zafi, lamarin dake kara matsalar cutar sankarau da yanzu haka ta hallaka jama’a da dama a kasar.